About Us

Tuesday, 8 November 2016

RAYUWAR TALAKA A JIHATA

Daga Adamu Bala Dansidi

KARATU A TURBAR MUTUWA.

lalle talaka na cikin kalu bale a wannan jiha tamu, talaka yana karatu karkashin mutuwa, su kuma hanya ne a gabansu mai dankaren tsada wanda an sare mana bishiyoyi don musamu kwararowar hamada ba'a maida mana wasu ba gashi talaka yana karatu babu bencin zama gina yana faduwa amma duk ba damuwar gwamnatin jiha bane.

Gaskiya wannan jihar inaga mulkin soja akeyi ko kuma mulkin mallaka, don demokaradiya akwai 'yancin fadin albarkacin bakinka amma wannan idan kafada sai albashinka ya tsaya ko kuma wani abu na dabam. Wannan wane irin mulki ne haka , bayan duniya fa akwai lahira, hisabi kuma gaskiya wallahi babu abinda ba abin tambaya bane a ranar kiyoma, amma karara kowa nagani ga bukatun al'umma amma ayi musu tilas kai jama'a anya kuwa wannan mulkin ???

1 comment:

  1. Allah ya sauwaka. Wannan Lamari yana neman ya gagari kundila

    ReplyDelete