About Us

Wednesday, 30 November 2016

ALLAH KA KWACE MU!!!

DAGA FMC AZARE.

tabbas wannan ba karamin ta'adi bane daina zuwan DR. SHEHU TABAWA BALEWA, wanda kwararren likitan fata ne wanda ke aiki a AKTH KANO yake zuwa locom FMC AZARE yakai shekara goma sha hudu (14years )yana zuwa wannan asibitin,  babu dalilin da za'ayi wata goma ba'a biyashi ba ko fiye da haka yayi hakuri yakai sau biyar akan kin biyansa kudin sa, kamar yadda yake zuwa yakan ga marasa lafiya kusan dari duk ranar laraba wannan kashe gari ne, miyasa sai a gwamnatinka ake samun wannan matsalar a wannan asibitin??? ace likitotin da suke zuwa duk sun daina zuwa don rashin iya mulki, gaskiya bazamu yarda ana zaluntar mutanenmu na kasar katagum dama Yobe da kuma mafi kusa damu da suke zuwa ganin wannan likitan daga garuruwa mabanbanta.

ABINDA YADARU YAU TSAKANIN LIKITAN FATA DA HUKUMAR FMC AZARE.

yau take laraba 39/11/2016
misalin 10:30am akan hanyarsa ta zuwa garin Azare sai yasamu matsala ta lalacewar mota daga kan hanyarsa zuwa Azare a yau laraba, yakira FMC Azare akan ayi masa agaji don daukansa don yabar tasan don gyarawa amma shiru babu wanda aka tura masa don daukansa, yayi kokari ya'iso duk da hakan shine kebin bashin kudi na watanni da yawa ba'abiyashi ba amma akamar haka, bayan yafara ganin marasa lafiya sai ya turo daya daga cikin Health Attendant akan ya sanar duk maison ganinsa daga yau yaje Bauchi ko Birnin Kudu ko kuma yatafi AKTH Kano wannan sanarwa ta kidima marasa lafiya sai daya daga cikin dattijan yashiga gunsa akan miyake faruwa shine ya labarta wannan labarin akan ga abinda akemar tun fil'azal.
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN.
wallahi na kidima dajin wannan labarin don duk mai kishin katagum yasan wannan cibayane ga cigaban garin dole duk mai fada aji yashiga wannan maganar don talaka yana cikin rudani bayyananne wanda indai akabar wannan abinda ke faruwa cikin wannan asibitin to babu kowa kenan agarin wanda ya saura .

YA ALLAH KASA WANNAN YAZAMA MAGANA TA KARSHE TSAKANINMU DA WANNAN SHUGABAN ASIBITIN DON GYARA WA'YANNAN MATSALOLIN GABA DAYA.
MUNA ROKON ALLAH DA YA SANJA MANA WANNAN MUTUMIN IDAN DAI BAMAI GYARUWA BANE.

No comments:

Post a Comment