About Us

Sunday, 6 November 2016

KIRA NA MUSAMMAN

DAGA ABD AZARE

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN.

A jiya ne da misalin goma da rabi zuwa sha daya na rana mukasami labarin hatsarin mota a garin Shu'arin na (Homa) wanda ta tashi daga garin Azare mai dauke da mutane goma sha biyar (15) a cikinta na fashewar taya .
Motar tana dauke da :-
1.'Ya'yan Limamin gari guda biyu wato Malam Ayuba
2. Jikanun Mai dawan Katagum 'ya'yan Ali Emier guda uku.
3. Matar Bar. Tata Sa'ad .
4. Maluma Hafsatu dake Gadau.
5. Wani bakanike .
6. Driver.
7. Wani matashi .

A lokacin da abin yafaru sakamakon fashewar taya mutane hudu suka mutu, daya 'yar gidan Ali Emier ,matar garin Gadau, Bakaniken, da kuma wani guda daya.

Sauran ansamu tahowa dasu Azare cikin FMC Azare , donyin magani, abinda nagani wanda yadawo da hankalina kan yazama wajibi ayi magana shine.

MASU WANNAN MOTOCI DA KUNGIYAR DREBOBI.
Gaskiya fa guda daya ne dole mugaya wa kanmu ita abinda na fahimta shine yawancin masu tuka motar nan matasa ne , kuma abin takaicin yaran motar ne ba ainihin direbobin ba, miyasa? Kuma wallahi babu hankali cikin yadda yawancinsu sukeyin tukin motar wanda ni dinnan shaida ne wani yaro wata rana kadan yahana na mareshi don yana ganganci damu kuma yana waya. Kira ga kumgiya da masu motocin wajibi ne garesu su zauna su tsawatar don hatsarin da akeyi daga Shu'arin zuwa Kano da gaba daya hamyar gaskiya yawancin su gudu ne yakeyin yawa, wanda ita motar ance idan abu zai faru kulle kanta takeyi, mu ceci 'yan uwanmu don a jiyama najiyo driver na motar yana labarin wai anamar fitila amma bai dauka wani abu bane, to koma dai minene wajibi ne mutsawatar a kanmu.

MASU SHIGA MOTAR .

Babu dalilin kuna cikin motar kuzama masu gaggawa don kawai zanje Kano na dawo a ranar zamu zuba ido ayi ta gudun ganganci damu, wajibine mugaya wa kanmu gaskiya mu tsawatar a driver din na yawan gudun da yakamata ace yanayi.

HUKUMOMIN DA HAKKIN YA DORU A KANSU .

Doka bata yarda da gudu mai yawa ba wanda wajibine ga hukumar ta ceci al'umma don gudun yana fita daga runanin mu, ayi kokari tsakanin hukumar dake garin Azare da wanda take garin Dutse don hada kai a ceci mutane don kune kadai wanda dokar take hannun ku, idan abu yayi tsamari kusaka tara mai yawa babu lamani wanda hakan zan saka don dole kuceci al'umma idan abun yaki yiyuwa ku hada da hukumar dake garin Kano don dai ceton al'umma don abin yayi yawa wallahi, Allah yakai korafinmu gunda zaiyi amfani.

KIRA GA HUKUMAR ASIBITI DAKE GARIN AZARE (FMC AZARE )

Gaskiya (A&E) tayi kadan a garin Azare don ankawo Emergency ajiyama da takai awa uku kafin tasamu kulawa, bayan gurin yayi kadan na fahimci akwai karancin ma'aikata wanda hakan ne zai jawo rashin kulawar, na tabbata akwai yadda zatayi da wannan matsalar da muka kawo, asali ma yadda aka ginashi akwai matsala don tun asali ma yayi kadan a Azare balle yanzu, Hukumar ta shiga ta cecemu don Allah don jiya naga dole sai sallamar wanda yake da dama dama akeyi don asaka wanda yafishi matsala, wanda shima yana bukatar ace a asibiti yake don bai gama warkewa ba don naga wajen shida wanda dibansu akayi ba da kafarsu suka fita ba gaskiya aduba wannan don ceton rayuwar al'umma .

No comments:

Post a Comment