About Us

Friday, 11 November 2016

JAN KUNNE

Via:  Lawal Muazu Bauchi

         On Facebook

Ya kamata matasa a Arewa su gane cewa rayuwarsu da ta 'ya'yansu Gwamnoninmu suke sayarwa to irin wadannan abubuwa da suke yi. Ko dai mu canza irin wannan halayyar ko rayuwar 'ya'yanmu tafi namu muni, Allah ya kyauta.

Ba yadda za'a yi ace kuna gani wani mutum ya zo, bai gina muku Makarantu ba in da yaranku zasu yi ilimi ba, bai horas da malamai da zasu na koyar da 'ya'yanku ba, bai horas da likitoci da maaikatan jinya ba, bai gina muku asibitoci ba, bai wadatar da ku da ruwan sha mai tsabta ba

Ba ruwan shi da tsaronku ko ta dukiyarku sannan ku zo Facebook kuna kare shi don yayi alkawarin gina masallatai 90, ko ya nada masu ba shi shawara 312 ko don ya sayi makara 3000.

Abin takaici shi ne, shi wanda ya baku Android ya saya muku data diyanshi suna turai suna karatu. Da zarar sun dawo, za'a basu aiki a CBN, SEC, NDIC, NNPC, FIRS da wasu wurare da ake ganin masu romo ne.

Ku kuma za'a barku da surutu a Facebook kamar yadda muke yi yanzu. Siyasar dimokuradiyya ta baku dama a kowane bayan shekara hudu ku canza shugabanni da ba su muku aiki ba. Amma in kun ce za ku ci gaba da biyewa wadannan mutane, to har abada ba ku rabo da kangin talauci da bauta ba

Ina fata matasanmu za su fahimci haka. Duniya ta tafi ta barmu a baya, saboda irin wadannan mutane da muka sa a gaba, wadanda ba abin da suka sa a gaba sai kyautatawa kawunansu dana iyalansu. Mu tashi mu farka 'yan Arewa.

No comments:

Post a Comment