Daga: Kalil Mustapha Katagum
BAKAN GIZO GIDAN YAUDARA.
DAGA MAI TATTAKI DAGA AZARE ZUWA BAUCHI LOKACIN CIN APC KUJERAR GWAMNA.
Mal. Nuhu dake Ungawar Makara-huta dake garin Azare, matashi ne wanda ya dau alkawari zaiyi tafiyar kafa daga Azare zuwa Bauchi matukar M.A Abubakar yaci kujerar mulkin jihar Bauchi wato (APC) cikin ikon Allah APC ta kafa mulki Mal. Nuhu ya daura aniyar tafiya yakama hanya yafara tafiya cikin ikon Allah yashiga garin Bauchi, sai yayi rashin dace General Tijjani Gamawa ya hadashi da Bakangizo akan yayi masa masauki, Bakangizo yakaishi APC Secreteriat dake jihar Bauchi ya bashi dubu biyu (#2,000 ) akan yaci abinci zaije yadawo yayi zama har yagaji akan Bakangizo zai dawo idan yagama zaikaishi wajen mai girma gwamna shiru , yaro yayi kira har yahaji Bakangizo yaki dauka , Hon. Tijjani Aliyu yazo akan zai tafi dashi sai yacemar ai Bakangizo yake jira rashin sani yafi dare duhu sai Tijjani yace to ga wannan kaci abinci mayi magana daga baya, bayan tafiyar Tijjani yaro yayi kiran Bakangizo daya zuwa biyu yaki dauka na uku sai ya kulle wayarsa, sai yaro yakira General Tijjani Gamawa yagayamar yadda sukayi sai yace Allah sarki ba'a kyautama ba, amma kasan gidan Sen. Nazif yace yana zuwa daga zuwansa Sen. Yace shine yaron General yace haka bayan yahuta Sen. Nazif yace aje abashi Babur na hawa sabo fil, yakuma ce ga dubu goma yayi kudin mota, daga nan yakira Hon. Tijjani yazo yabashi dubu ashirin (#20,000) .
Kuma har mahaya sukayi rashin dace suka fada hannun sa abisa wasan dawaki, wanda yaki kyautatawa wanda yayi tafiyar kafa ne zai yi wa wanda yayi wasan doki, tabbas wannan shine yadda akayi da Bakangizo mai shanye ruwa.
Daga karshe muke neman hakkin mutane biyu daga gurin Bakangizo kuma jagoran masu wassani da al'adu na jihar Bauchi, wanda yake da wannan ne zaiyi takara cikin garin mu , Allah ya kyauta kadan daga cikin labaren kenan kafin muyi magana ta biyu.
No comments:
Post a Comment